Zamu nazarci yadda za mu yi amfani da Hazard a wasan yau - Zidane
Wallafawa ranar:
Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya tsegunta cewa Eden Hazard zai samu fafatawa na dan lokaci a wasan gasar zakarun nahiyar Turai da za su kara da Borussia Monchengladbach a Talata.
Hazard ya yi ta fama da rauni tun da ya koma Santiago Bernabeu daga Chelsea a shekarar 2019, kuma ya buga wasanni 22 ne kawai, inda ya saka kwallo daya a raga.
Dan wasan na kasar Belgium ya samu koma baya, bayan da ya sake jin wani rauni a farkon wannan kaka yayin da yake buga wa Real Madrid.
Ko a wasan hamayya na El Clasico da Madrid ta lallasa Barceona har gida a Asabar da ta gabata an ga Hazard a bayan fage, yana shirin fadawa fili amma har aka tashi bai buga ba.
Amma Zidane yana cewa ganin Hazard na nuni da cewa ya samu sauki, kuma za su yi nazari kan yadda zasu yi amfani da shi a wasan yau Talata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu