Wasanni

Klopp ya fusata da raunin Fabinho a karawar Liverpool da Midtjylland

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool  Jurgen Klopp.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp. Reuters/Jason Cairnduff

Mai horar da kungiyar kwallon kafa Liverpool Jurgen Klopp ya harzuka matuka da raunin dan wasan tsakiyar kungiyar Fabinho yayin karawarsu da Midtjylland karkashin wasannin cin kofin zakarun Turai.

Talla

Fabinho dan Brazil ya bi sahun Virgil van Dijk da Joel Matip dukkanninsu masu tsaron bayan Liverpool da ke ci gaba da jinya, wanda ke matsayin babban kalubale ga tsaron bayan kungiyar dai dai lokacin da wasannin sabuwar kaka suka kankama.

A kalaman Jurgen Klopp bayan tashi daga wasan na jiya da Liverpool ta yi nasara da kwallaye 2 da nema, ya ce sam raunin na Fabinho ba shi suka yi fata ba.

Kafin yanzu dai Klopp na amfani da Fabinho ne don cike gurbin Van Dijk wanda ya samu rauni tun ranar 17 ga watan nan yayin karawarsu da Everton hakan kuma na e nuna cewa raunin na Fabinho a yanzu zai sanya Klopp a tsaka mai wuya wajen laluben wanda zai cike gurbin ‘yan wasan biyu masu matukar amfani ga tawagar.

Yanzu haka dai matashin dan wasan na Liverpool mai shkearu 19 daya dawo daga aro, Rhys Williams ne zai hada karfi da Joe Gomez wajen rike bayan kungiyar.

Ko a bara Jurgen Klopp ya koka da yadda ake yawan jikkata masa ‘yan wasa ba kuma tare da daukar mataki ba akai daga hukumomi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.