Liverpool za ta sauya salon wasanta saboda karancin masu tsaron baya
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya sanar da shirin sauya salon zubin ‘yan wasansa a fili saboda raunin uku daga cikin masu tsaron bayan tawagar.
Wallafawa ranar:
Liverpool mai rike da kambun Firimiya tun a wasan farko na wannan kaka ‘yan wasanta suka fara samun raunin da ya tilasta su zaman jinya, ciki kuwa har da mai tsaron ragarta lamba daya Alisson Becker da kuma Kaftin dinta wato Jordan Henderson, ko da ya ke tuni suka murmure tare da dawowa fagen tamaula.
Sai dai raunin masu tsaron bayan 3 wato Joel Matip Virgil van Dijk da kuma Fabinho a baya-bayan nan ya tilastawa Jurgen Klopp kwaikwayon salon da Pep Guardiola ya yi amfani da shi Barcelona lokacin da ya fuskanci makamanciyar matsalar, don kai labari a wasannin wannan kaka.
Yanzu haka dai Liverpool za ta yi amfani salon Tiki Taka maimakon gegenpressing da ta ke amfani da shi tsawon shekaru 3 karkashin Jurgen Klopp inda sabon dan wasanta Thiago Alcantara zai yi matukar amfani a salon, musamman kasancewarsa mai karsashin wajen saurin bayar da kwallo kuma shi dama salon na tiki taka na bukatar ‘yan wasa masu saurin bayar da kwallo, salon da kuma zai takaitawa ‘yan wasan tsakiya aiki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu