Wasanni-Kwallon kafa

Ronaldo ya warke daga cutar korona bayan kwanaki 19

Cristiano Ronaldo na Portugal da ke taka leda a Juventus.
Cristiano Ronaldo na Portugal da ke taka leda a Juventus. REUTERS/Massimo Pinca

Kungiyar kwallon kafar Juventus ta sanar da cewar tauraron 'dan wasan,ta Cristiano Ronaldo ya warke daga cutar koronar da ta kama shi bayan kwanaki 19.

Talla

An dai gano Ronaldo ya harbu da cutar ce a ranar 13 ga watan Oktoba lokacin da ya je yi wa kasarsa ta Portugal wasa a gasar Turai, abinda ya sa ya killace kansa tun bayan komawa kasar Italia.

Kungiyar Juventus ta ce gwajin da aka sake yiwa fitaccen ‘dan wasan na duniya ya nuna cewar yanzu haka baya dauke da cutar ta korona, abinda ke nuna cewar ya warke kuma babu bukatar ci gaba da killace kan sa.

Ronaldo bai samu damar bugawa Juventus wasa ba lokacin da kungiyar sa ta kara da Barcelona a gasar cin kofin zakarun Turai wanda suka sha kashi da 2-0 da kuma wasan Dynamo Kiev da suka samu nasara da ci 2-0.

Dawowar Ronaldo fagen wasa zai baiwa kungiyar Juventus dake karkashin Andrea Pirlo damar samun Karin tagomashi ganin yadda yanzu haka take matsayin na 5 a gasar Serie A, wadda AC Milan ke jagoranci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI