Arsenal ta doke Manchester United har gida da kwallo 1 mai ban haushi
Kungiyar Arsenal ta bi Manchester United har filin kwallon ta da ke Old Trafford inda ta doke ta da ci 1 mai ban haushi a wasan firimiya da aka kara yau.
Wallafawa ranar:
Dan wasan gaba na kungiyar Pierre-Emerick Aubameyang ya jefa kwallon guda da Arsenal ta ci ta hanyar bugun fenariti a misalin minti 69 bayan da Paul Pogba ya taka Hector Bellerin a gaban gidan su.
Wannan kwallon ya kawo karshen wasanni biyar da Aubameyang ya yi ba tare da jefa kwallo ba.
Wannan nasara ta bai wa Arsenal damar tara maki 12 da kuma zama na 8 a teburin firimiya wadda kungiyar Liverpool ke jagoranci da maki 16.
Sauran wasannin da akayi yau sun nuna cewar Southampton ta doke Aston Villa da ci 4 da 3, Newcastle ta doke Everton da ci 2 da 1.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu