Barcelona ta yi wasa 4 a jere babu nasara
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta doka wasanni 4 a jere ba tare da samun nasara ba, abinda ke dada jefa shakku kan irin shirin da tayi a gasar kakar bana.
Wallafawa ranar:
A karawar da kungiyar tayi daren jiya da Alaves a gasar La Liga, kungiyar ta yi kunnen doki duk da cewa Alaves ta karkare wasan ne da ‘yan wasa goma sakamakon korar da alkalin wasa ya yiwa Jota.
Luis Rioja ya jefawa Alaves kwallo, kafin daga bisani Barcelona ta farke ta hannun Antoine Griezmann, abinda ya bata maki guda a wasan da kuma gurbi na 12 a teburin La Liga da maki 8, duk da yake tana da kwantan wasanni guda biyu.
Real Madrid ke jan ragamar tebur da maki 16 da kuma kwantan wasa guda yayin da Real Sociedad da Atletico Madrid da Cadiz ke matsayi na 2 da 3 da 4 da maki 14 kowacce daga cikin su.
A wasannin jiya Real madrid ta lallasa Huesca da ci 4-1, Atletico Bilbao ta doke Sevilla da ci 2-1, sai kuma Atletico Madrid da ta doke Osasuna da ci 3-1.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu