Ronaldo ya jefa kwallaye 2 bayan warkewa daga cutar Korona
Tauraron kwallon kafar kasar Portugal da Juventus, Cristiano Ronaldo ya jefa kwallaye 2 a karawar da kungiyar sa ta Juventus ta yi da Spezia a gasar Serie A wanda suka lashe da ci 4-1.
Wallafawa ranar:
Wannan shine karo na farko da Ronaldo ke wasa bayan warkewar da yayi daga cutar korona wadda ta sanya shi killace kan sa na kusan makwanni biyu.
Ronaldo ya shiga wannan wasan ne bayan minti 56 inda ya maye gurnin Paulo Dybala, ya kuma jefa kwallon farko mintina 3 bayan shigar sa kafin ya kara ta biyu ta bugun fenariti.
Bayan kammala wasan Ronaldo ya shaida wa manema labarai cewar, ‘Ronaldo ya dawo. Wannan shine abu mai muhimmanci’.
Dan wasan ya ce an dakatar da shi wasa na dogon lokaci duk da yake baya jin wani ciwo a jikin sa, amma ga shi yau ya dawo yana abin da yake son yi, wato buga wasan kwallon kafa.
Wannan nasara ta baiwa Juventus damar komawa ta biyu a teburin Serie A wadda kungiyar AC Milan ke jagoranci.
Shima Zlatan Ibrahimovic ya jefa wata kwallo ta ban mamaki a wasan da kungiyar AC Milan ta samu nasara a kan Udinese.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu