Wasanni

Maradona ya cika shekaru 60 da haihuwa

Sauti 09:07
Diego Armando Maradona.
Diego Armando Maradona. Reuters/Muhammad Hamed

A cikin shirin 'Duniyar wasanni' na wannan mako, Abdurrahman Gambo Ahmad, ya yi mana dubi na musamman a game da cikar tsohon shahararren dan wasan kwallon kafa na duniya, Diego Armando Maradona shekaru 60 da haihuwa. Wannan gwarzon dan wasan kwallon kafa, dan kasar Argentina, ya yi fice ne a gasar cin kofin duniya d aka yi a Mexico a shekarar 1986, inda ya taimaka wa kasarsa ta lashe kofin.