Maradona ya fara murmurewa bayan tiyatar kwakwalwa
Fitaccen dan kwallon Duniya Diego Armando Maradona na murmurewa daga tiyatar da aka masa na cire gudan jinin da ya makale a kwakwalwar sa kwanaki bayan ya cika shekaru 60 da haihuwa.
Wallafawa ranar:
Likitan sa Leopoldo Luque ya bayyana cewar kwararrun likitoci a asibitin Buenos Aires suka kwashe minitina 80 suna yiwa tsohon tauraron dan wasan aiki kafin cire jinin.
Rahotanni sun ce an kai Maradona ne asibitin La Pata, garin da ya ke aikin horar da kungiyar Gimnasiay Esgrima ranar litinin bayan ya yi korafi dangane da halin lafiyar sa, kuma gwajin da likitoci suka masa ya nuna jinin da ya makale a kwakwalwar ta sa.
Tsohon tauraron ya yi fama da bugun zuciya sau biyu da cutar hanta da na matsarmama a baya.
Tauraron kungiyar Barcelona Lionel Messi ya aike masa da sakon fatan alheri da kuma warwarewa cikin sauri.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu