Wasanni

Ni na fi dacewa na horas da Manchester United-Solksjaer

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solksjaer ya ce, ba zai fadi ba kamar yadda gajiyayyen gini ke zubewa bayan ya sha kashi jere da juna, yana mai cewa, shi ne dai ya fi cancantar horas da kungiyar.

Ole Gunnar Solskjaer
Ole Gunnar Solskjaer REUTERS/Andrew Yates
Talla

Daga cikin kashin da ya sha a baya-bayan nan har da dukan da Basksehir ta yi wa kungiyarsa a gasar cin kofin zakarun Turai.

Tuni Manchester United ta tuntubi tsohon kocin Tottenham Mauricio Pochettino game da daukarsa domin maye gurbin Solksjaer.

Akwai yiwuwar Manchester United ta mika masa takardar sallama muddin ya gaza doke Everton a karawar da za su yi a gobe a gasar firimiyar Ingila.

Kodayake wasu bayanai na cewa, watakila Manchester din ta sake ba shi wata dama koda kuwa ya yi rashin nasara a wasan na gobe, musamman ganin yadda yake dasawa da jiga-jigan kungiyar ta Old Trafford kamar yadda Sky Sport ta rawaito.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI