Wasanni-Kwallon kafa

Hazard da Casemiro na Madrid sun kamu da korona

kungiyar Real Madrid dake Spain ta sanar da cewar biyu daga cikin 'yan wasan ta Eden Hazard da Casemiro sun harbu da cutar korona wadda ta sake farfadowa a nahiyar Turai.

Eden Hazard dan wasan Real Madrid da ya harbu da korona.
Eden Hazard dan wasan Real Madrid da ya harbu da korona. © REUTERS/Sergio Perez
Talla

Sanarwar da kungiyar ta fitar yau da safe ya bayyana cewar yan wasan su guda biyu sun harbu da cutar bayan gwajin da aka musu jiya juma’a, yayin da gwajin ya tabbatar da cewar sauran ‘yan wasan kungiyar da masu horar da su da ma’aikata basa dauke da ita.

Saboda haka kungiyar tace wadannan ‘yan wasa guda biyu ba zasu shiga wasan da Madrid zata kara da Valencia gobe lahadi ba, kuma babu wanda zai je yiwa kasar sa wasa a makon gobe saboda za’a killace su kamar yadda doka ta tanada.

Mai horar da ‘yan wasan Kungiyar Zinedine Zidane ya bayyana cewar ‘yan wasan biyu na cikin yanayi mai kyau duk da duk da hankalinsu ya tashi dangane da rahoton harbuwa da cutar.

Kafin dai wadannan ‘yan wasa guda biyu kungiyar ta sanar da cewar Eder Militao dan kasar Brazil shi ma ya kamu da cutar a ranar Litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI