Wasanni-Kwallon kafa

Kocawan Firimiyar Ingila na so a dawo da dokar canjin 'yan wasa 5

Masu horarawa a gasar kwallon kafar Firimiyar Ingila na iya neman a sake dawo da dokar canza ‘yan wasa da suka kai 5 a wannan kaka, duk da cewa sau biyu ana watsi da dokar.

Kwallon kafa a cikin filin wasa, a gasar Firimiyar Ingila.
Kwallon kafa a cikin filin wasa, a gasar Firimiyar Ingila. REUTERS/Nigel Roddis
Talla

Kocwa a gasar da dama sun nuna rashin jin dadinsu ganin cewa suna iya yin canji 3 ne kawai a kaka 2020 da 21, bayan an bari suna yin canji da ya kai 5 a lokacin da aka dawo karawa a kakar da ta gabata.

Gasar Firimiyar Ingila ce kawai ta koma yin canji 3 a cikin manyan gasannin kwallon kafa a fadin duniya.

Wasu manyan kocawa a gasar dai sun yi zargin cewa canji 3 da ake yi a halin yanzu shine ummul’aba’isan yawan rauni da ‘yan wasan Firimiya ke yawan samu.

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp da takwaransa na Manchester City Pep Guardiola duk sun ce yawan rauni da ‘yan wasa ke samu a jijiyoyinsu na aukuwa ne saboda karancin canji na ‘yan wasa yayin fafatawa.

Rahotanni na nuni da cewa sau 2 ana mika wa kungiyoyin gasar firimiya 20 wannan batu amma suna nuna rashin amincewa, duba da yadda tayin ba ya samun amincewar kungiyoyi 14 da da ake bukata.

Kocin West Ham, David Moyes a ranar Juma’a ya ce ya canza ra’ayinsa a game da batun, bayan yin fatali da shi tun da farko.

Sai dai a nasa bangaren kocin Aston Villa Dean Smith, yana ganin kamata ya yi gasar ta tsaya ga canji 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI