Wasanni-Kwallon kafa

Pogba ba ya jin dadin Manchester United - Deschamps

Mai horar da ‘yan wasan tawagar kwallon kafar kasar Faransa, Didier Deschamps ya ce ba ya tsammanin Paul Pogba yana jin dadin halin da yake ciki a yanzu a Manchester United.

Paul Pogba na Manchester United
Paul Pogba na Manchester United Reuters/Jason Cairnduff
Talla

Pogba mai shekaru 27  ya sha fama da matsalar rashin samun gurbi a cikin masu soma wa kungiyar wasa a ‘yan watannin nan saboda da mastalolin rauni da ya samu da kuma harbuwa da cutar coronavirus da dai sauran matsaloli.

A wannan kaka, sau 2 ne kawai Pogba ya buga wa United wasa na tsawon mintuna 90, kuma sunewasannin da  Tottenham da Arsenal suka doke su; kuma kwallo daya tilo da ya samu ya saka a raga ita ce a wasa tsakanin United da Brighton a gasar cin kofin Carabao.

Dan wasan bai tabuka komai ba ko a wasan da ya buga wa Faransa a baya bayan nan kuma Deschamps ya kare shi inda yake cewa ba ya kan ganiyarsa ne.

Deschamps ya ce ba shi da wata shawara da zai ba dan wasan ganin cewa ya lakanci kungiyarsa da ma ‘yan wasansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI