Wasanni

Juventus za ta sallami Ronaldo saboda wahalar dawainiyarsa

PSG ta Faransa na shirin taya dan wasan Portugal mai taka leda a Juventus, Cristiano Ronaldo muddin kungiyarsa wadda ke Italiya ta tsayar da shawarar sayar da shi a kaka mai zuwa.

Cristiano Ronaldo.
Cristiano Ronaldo. Ảnh REUTERS
Talla

Yanzu haka Ronaldo na karbar albashin Euro miliyan 28 a kowacce shekara a kungiyar wadda ita ce zakarar gasar Serie A.

Rahotanni na cewa, Juventus na son raba gari da Ronaldo domin rage yawan kudin da take kashewa a kansa.

Sai dai tuni shugaban PSG, Leonardo ya ce, suna son dan wasan mai shekaru 35, inda ya bayyana cewa, za su iya daukar dawainiyarsa duk da cewa, annobar coronavirus ta taba tattalin arzikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI