Wasanni

Shugaban FA ya yi murabus saboda bakaken fata

Greg Clarke
Greg Clarke Reuters

Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Ingila, Greg Clarke ya yi murabus bisa wasu kalamai da ya furta da ake ganin tamkar na nuna wariyar launi ne ga bakeken fata masu taka leda a Ingila.

Talla

Clarke ya fahimce cewa, ya yi kuskure kan yadda ya yi amfani da kalmar '‘yan kwallo masu launi' a yayin ganawarsa da mambobin Kwamitinin Kula da Al’adu da Kafafen Yada Labarai har ma da Wasanni na Majalisar Dokokin Ingila.

Ya gana da majalisar ne domin tattaunawa kan matsalar nuna wariya da ake yi wa wasu ‘yan wasa a shafukan sada zumunta.

Dan majalisa, Kevin Brennan ne ya tilasta wa Clarke neman afuwa saboda wadannan kalaman da ka iya harzuka wasu.

Kodayake Clarke ya ce, ya fadi haka ne ba da wata manufa ba kuma ya yi matukar bakin cikin aikata wannan kuskuren a cewarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.