Zan karya tarihin Yakini na cin kwallaye - Osimhen
Dan wasan gaba ba Napoli, kuma dan Najeriya Victor Osimhen ya bayyana aniyarsa na zarce irin banjintar da Rashidi Yekini ya yi a wajen cin kwallaye a babbar tawagar kwallon kafar kasarsa ta Super Eagles duk da cewar 'kamar da wuya'.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Har yanzu dai babu dan wasan Najeriya da ya kai Yekini saka kwallo a raga, inda ya zura kwallaye 37 daga wasanni 58, kuma ya taimaka wa tawagar ta taka rawar gani a gasannin kasa da kasa.
Ya zuwa yanzu, Osimhen ya zura kwallaye 3 ne a raga daga cikin wasanni 9 da ya buga wa Najeriya tun da ya fara wa tawagar Super Eagles wasa a shekarar 2017.
Dan wasan mai shekaru 21 ya bayyana cewa zai ci gaba da aiki tukuru don ganin ya zama dan wasan da ya fi ci wa tawagar Super Eagles ta Najeriya kwallo a tarihi, sai dai ya ce lallai ba abu ne mai sauki ba.
Ana sa ran Osimhen ya taka mahimmiyar rawa a karawar da za ta gudana tsakanin Najeriya da Sierra Leone a Juma’ar nan a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu