Wasanni

An fara gasar kwallon kafa ta mata zalla a Saudiya

An fara gudanar da gasar kwallon kafa ta mata zalla irinta ta farko a Saudiya bayan an jinkirta ta saboda annobar coronavirus.

'Yan matan Saudiya da suka yi layi domin shiga filin wasa na birnin Jeddah.
'Yan matan Saudiya da suka yi layi domin shiga filin wasa na birnin Jeddah. AFP
Talla

Sama da ‘yan wasa 600 daga kungiyoyin biranen Riyadh da Jeddah da Dammam ke fafatawa a wannan gasa ta cin kofin zakaru.

Kodayake ba a haska wasan farko a kafar talabijin ba wanda aka fara shi a yammacin jiya Talata , amma kafafen yada labaran kasar sun jinjina wa ‘yan matan da suka shiga harkar wasanni domin a dama da su.

A shekarar 2018 ne aka fara bai wa matan Saudiya izinin shiga filayen wasanni domin kallon kwallon kafa kai tsaye a kasar.

An dai kwashe tsawon shekaru da dama, mahukuntan Saudiya na hana mata shiga harkokin wasanni bisa dalilai na addini da al’ada, inda malaman kasar suka gargadi cewa, bude fileyen wasannin ga ‘yan matan ka iya gurbata tarbiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI