Wasanni

FIFA ta dakatar da shugaban CAF Ahmad Ahmad na shekaru 5 saboda rashawa

Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta dakatar da shugaban hukumar kwallon kafar Afrika Ahmad Ahmad na tsawon shekaru 5 bayan samunsa da laifukan almundahanar kudade da kuma karbar rashawa.

Dakataccen shugaban hukumar kwallon kafar Afrika CAF Ahmad Ahmad.
Dakataccen shugaban hukumar kwallon kafar Afrika CAF Ahmad Ahmad. MOHAMED EL-SHAHED / AFP
Talla

Cikin sanarwar da FIFA ta fitar yau Litinin ta ce Ahmad Ahmad dan Madagascar zai kuma biya tarar dala dubu 220, bayaga haramcin na shiga harkokin gudanarwar wasannin na Afrika har tsawon shekaru 5.

Tun a watan Maris din shekarar 2017 ne Ahmad Ahmad ya yi nasarar darewa kujerar shugabancin hukumar ta CAF yayinda kuma yak e neman wa’adi na biyu a 2021.

Acewar FIFA Ahmad Ahmad ya yi mata zamba cikin amince ta yadda ya ci amanar yadda da ta kais hi kujerar shugabancin ta hanyar karbar nagoro da kuma azurta kanshi da kudaden kula da harkokin kwallon kafar Nahiyar.

Yanzu haka dai Ahmad Ahmad mai shekaru 50 na da damar daukaka kara kan hukuncin na FIFA a kotun sauraren karakin wasanni ta CAS.

Ko a cikin watan Afrilun bara, tsohon jami’in hukumar ta CAF aMR Fahmy ya aikewa FIFA wasikar da ke zargin Ahmad Ahmad da karkatar da wasu kudade karbar rashawa da kuma cin zarafi da muzgunawa jami’in hukumar musamman mata, matakin da ya kai ga kameshi watanni 2 bayan zargin yayin gasar kwallon kafar mata da ta gudana a Faransa amma kuma aka sakeshi kwana guda bayan kamen.

Dama dai bukatar Ahmad Ahmad ta ci gaba da jagorancin CAF ya gamu da kakkausar suka daga shugaban hukumar kwallon kafar Senegal Augustine Senghor, yayinda shugaban hukumar kwallon kafar Mauritania Ahmed Yahya da Jacques Anouma na Ivory Coast kana attajirin Afrika ta kudu Patrice Motsepe dukkanninsu suka nuna bukatar tsayawa takara don neman kujerar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI