Wasanni-Kwallon kafa

Messi ba zai taka leda a karawar Barcelona da Dynamo Kyiv ba- Koeman

Ronald Koeman ya ce suna da duk makin da suke bukata a matakin rukuni-rukuni karkashin gasar ta cin kofin zakarun Turai.
Ronald Koeman ya ce suna da duk makin da suke bukata a matakin rukuni-rukuni karkashin gasar ta cin kofin zakarun Turai. REUTERS/Albert Gea

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Ronald Koeman ya cire sunan kaftin din tawagar Lionel Messi da dan wasan tsakiyar tawaar Frenkie de Jong daga jerin ‘yan wasansa da za su taka leda a karawar kungiyar da Dynamo Kiev a gobe Talata karkashin gasar cin kofin zakarun Turai.

Talla

A cewar kocin manufar ajje Messi da De Jong shi ne don basu damar hutawa dai dai lokacin da Barcelona ke jagorancin teburinta da maki 9 bayan doka wasanni 3 sama da Juventus da ke matsayin ta 2 da maki 6, ko da ya ke Barcelonar kuma na matsayin ta 12 a teburin La Liga can a cikin gida gida bayan shan kayen baya-bayan nan hannun Atletico Madrid da kwallo 1 mai ban haushi.

Mai horar da kungiyar ta Barcelona ya ce Messi da Frankie na bukatar hutu la’akari da cewa dukkanninsu sun doka ilahirin mintuna 90 na dukkannin wasannin Barcelona tun farkon kaka zuwa yanzu bugu da kari kuma Messi ya dokawa kasarsa wasanni 4 yayinda De Jong ya dokawa kasarsa wasanni 5 cikin ‘yan tsakanin nan.

Ronald Koeman ya sanar da cewa suna da dukkannin makin da suke bukata a gasar cin kofin zakarun Turai don zuwa mataki nag aba, wanda ke nuna cewa dole su tattala ‘yan wasansu don tunkarar wasannin gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.