Wasanni

Barcelona ta yi bajinta ba tare da Messi ba

Lionel Messi
Lionel Messi REUTERS/Albert Gea

Barcelona  wadda ta yi wasanta ba tare da Lionel Messi ba  ta samar wa kanta gurbi a matakin ‘yan 16 a gasar zakarun Turai bayan ta lallasa Dynamo Kyiv da kwallaye 4-0.

Talla

Duk da cewa Barcelona ta hutar da gwarzon dan wasan nata, amma yaran na Ronald Koeman sun nuna bajinta, yayin da kuma suka samu nasara a daukacin wasanni hudu da suka buga a matakin rukuni na gasar.

Sergio Dest ya fara yaga ragar Dynami Kyiv a minti na 52, yayin da Martin Braithwaite ya zura kwallaye biyu a mintina na 57 da 70, sannan kuma Antoine Griezman ya jefa kwallon karshe.

Messi na ci gaba da fuskantar kalubale a kungiyar kuma babu rashin tabbas game da makomarsa a Camp Nou, yayin da ya kusan raba gari da kungiyar a kakar da ta gabata.

Yanzu haka dan takarar shugabancin Kungiyar Barcelona, Victor Font ya ce, yana fatar shawo kan Messi don ganin dan wasan ya ci gaba da zama a Camp Nou.

Nan da kwanaki 59 masu zuwa za a gudanar da zaben shugabancin Barcelona, yayin da dan Font ke cewa, za a samu sabbin zubi a kungiyar.

Font na ganin cewa, akwai wasu abubuwa da Messi ke bukata don ci gaba da zama a Camp Nou kuma a cewarsa, zai samar da wadannan abubuwa don shawo kan dan wasan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.