Wasanni-Kwallon kafa

Fitattun 'yan kwallo sun fara aike da sakon ta'aziyyar Diego Maradona

Shararren dan kwallon kafar Duniya Diego Maradona.
Shararren dan kwallon kafar Duniya Diego Maradona. REUTERS/Charles Platiau

Taurarin 'yan wasan duniya na da, da na yanzu sun fara aikewa da sakon ta’aziyyar rasuwar Diego Maradona, tsohon dan wasan Argentina da ya yi fice a duniya, wanda ya rasu da yammacin yau Laraba.

Talla

Daga cikin wadanda suka aike da sako harda babban abokin hamayyarsa Pele na Brazil, wanda ya bayyana alhinin rashin abokin na sa, kuma gwarzo, sai kuma Michel platini da ya ce sun yi asarar wani sashe na tarihinsu.

Sauran wadanda suka yi tsokaci kan mutuwar sun hada da Lionel Messi, kaftin din Argentina da kungiyar Napoli da Maradona ya daga darajar ta a duniya Javier Mascarano da kungiyar Bayern Munnich da Bryan Robson na Ingila da shugaban kungiyar kwallon kafar Turai Aleksander Ceferin.

Sauran sun hada da Peter Reid da Rio Ferdinand tsoffin Yan wasan Ingila da kuma kungiyar kwallon kafa ta Liverpool.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.