Wasanni-Kwallon kafa

Ibrahimovic na gab da komawa fagen dokawa kasarsa leda

Dan wasan AC Milan Zlatan Ibrahimovic.
Dan wasan AC Milan Zlatan Ibrahimovic. Daniele Mascolo/Reuters

Dan wasan gaba na AC Milan Zlatan Ibrahimovich ya bayyana cewa ya yi kewar bugawa kasarsa Sweden wasa, inda ya sanar da yiwuwar ya koma don bugawa kasar ta sa wasannin cin kofin kasashen Turai na EURO 2020 da ke tafe.

Talla

Ibrahimovich mai shekaru 39 wanda ya yi ritaya daga takawa kasarsa leda a 2016 bayan dawowa daga wasannin cin kofin Duniya, na wannan batu ne bayan karbar kyautar karramawa a matsayin zakaran kwallon kasar ta Sweden karo na 12.

Yayin zantawarsa da manema labarai bayan karbar lambar yabon ta karramawa, Ibrahimovich ya ce ko shakka babu ya yi kewar dokawa kasar ta sa leda amma yana bukatar lokaci don yin tunanin ko yana bukatar komawa fagen bugawa kasar tasa kwallo.

Zlatan wanda ya zura kwallaye 62 a wasanni 116 da ya bugawa Sweden, na ci gaba da nuna bajinta a sabon Club dinsa AC Milan inda ko cikin wannan kaka ya zura kwallaye 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.