Wasanni-Kwallon kafa

Tsohon Tauraron kwallon Duniya Diego Maradona ya mutu yana da shekaru 60

Shararren dan kwallon kafar Duniya Diego Maradona.
Shararren dan kwallon kafar Duniya Diego Maradona. REUTERS/Henry Romero

Shahararren dan kwallon Kafar Argentina, Diego Maradona ya rasu yau Laraba yana da shekaru 60 bayan fama da rashin Lafiya, kamar yadda kakakinsa ya sanar da kafafen yada labaran kasar.

Talla

Maradona, wanda Duniya ke kallo a matsayin daya daga cikin shahararrun 'yan kwallo da babu kamarsu, shi ne ya jagoranci tawagar kwallon kafar Argentina a matsayin Kyaftin da ta lashe kofin duniya a shekarar 1986 a Mexico.

Tuni dai shugaban kasar Argentina Alberto Fernandez ya sanar da makokin  kwanaki 3 a daukacin kasar don jimamin mutuwar Maradona wanda ya gamu da bugawar zuciya.

Kafafen yada labaran Argentina sun sanar da cewa tun da tsakar ranar yau Laraba jikin Maradona ya tsananta a gidansa da ke birnin Buenos Aires.

Diego Armando Maradona ya yi rayuwa ta shahara mai cike da kwan-gaba-kwan-baya da cece kuce, musamman ganin yadda ta’ammali da hodar ibilis da barasa fiye da kima ya yi tasiri a lafiyar dan wasan mai matukar kuzari da basira a harkar murza tamaula.

A farkon wannan wata, an yi wa dan wasan tiyata don cire gudan jini da ya yi kane kane a kwakwalwarsa.

Sau 3 Maradona yana kwanciya a asibiti a cikin shekaru 20 da suka wuce sakamakon matsalar rashin lafiya da ke da nasaba da mu’amalarsa da barasa da kuma muggan kwayoyi.

Diego Maradona ya ci sama da kwallaye 300 masu cike da bajinta, amma 2 daga cikinsu da suka fi shahara na da tazarar mintina 4 a tsakaninsu, kuma sun zo ne a ranar 22 ga watan Yunin shekarar 1986 a gasar cin kofin duniya da Mexico ta karbi bakonci.

Shekaru 4 kafin shekarar 1986, Maradona da Argentina ba su tabuka komai ba a gasar kofin duniya ba, inda aka yi waje da su a zagayen farko, amma a 1986, sun sauka Mexico ne da shirin bai wa mara da kunya.

A Mexico, Argentina sun doke dadaddun abokan hamayyarsu Uruguay a matakin kungiyoyi 16, sannan suka gwabza da Ingila a matakin daf da na kusa da karshe a katafaren filin wasa na Azteca.

Maradona ya sha nanata labarin karonsa da Ingila a littafin tarihin rayuwarsa da ya wallafa, musamman kwallon da ya jefa a ragar Ingila da hannu, wacce aka wa lakabi da ‘hannun Allah’.

Ya mutu a gidansa da ke birnin Buenos Aires sakamakon bugun zuciya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.