Wasanni-Kwallon kafa

Cavani ya nemi yafiya kan abin da ya wallafa bayan wasansu da Southampton

Edinson Cavani wanda ya sauya sheka daga PSG zuwa Manchester United a kakar wasan da ta gabata.
Edinson Cavani wanda ya sauya sheka daga PSG zuwa Manchester United a kakar wasan da ta gabata. JEAN-CHRISTOPHE VERHAEGEN / AFP

Dan wasan Manchester United Edinson Cavani ya nemi yafiyar jama’a kan wani sako daya wallafa ya kuma goge nan take inda cikin sakon ya yi amfani da wani salon Magana daya samo asali daga Spain kalaman da yakan iya zama batanci ko kuma nuna wariya a wani yaren.

Talla

Cavani dan Uruguay wanda ya wallafa sakon bayan nasarar tawagarsa ta lallasa Southampton da kwallaye 3 da 2 ya ce manufar sakon shi ne godiya ga abokinsa da ya taya shi murnar zura kwallo a pkarawar amma ba muzantawa kowa ba ko kuma nuna wariya ba.

Yanzu haka dai hukumar FA na bibiyar sakon don daukar matakin da ya kamata kan Cavani mai shekaru 33.

Manchester United ta wallafa cewa ta na da masaniya kan sakon na Cavani kuma bai wallafa don muzanta wani ba hasalima ya gaggauta gogeshi bayan da aka ankarar da shi cewa za a iya fassarashi da wata manufa daban.

Karkashin dokokin FA dai duk dan wasan da aka samu da laifin kalamai ko kuma sakon nuna wariya kai tsaye zai fuskanci dakatarwar wasanni 3 ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.