Wasanni-Kwallon kafa

Ba mu da isassun 'yan wasan tunkarar wasannin da ke gabanmu- Klopp

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool  Jurgen Klopp.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp. REUTERS/Charles Platiau

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce bashi da wadattun ‘yan wasan da zai yi amfani da su wajen sauye-sauye a karawar tawagarsa da Ajax yau Talata, dai dai lokacin da bayanai ke nuna Thiago Alcantara zai kai badi gabanin ya kammala murmurewa daga raunin da ya samu a gwiwa.

Talla

Jurgen Klopp ya sake samun karin majinyata ne bayan raunin James Milner a karawar Liverpool da Brighton ranar asabar din da ta gabata, wasan da suka yi canjaras da kwallo 1 da 1, inda Milner ya samu rauni a kafada.

A cewar Klopp damuwarsa ba wai gasar ta cin kofin zakarun Turai ba, babbar damuwarsa halin da ‘yan wasan za su shiga saboda babu masu sauyarsu a fili.

Mai horar da kungiyar ta Liverpool ya ce alfarmar da ya kamata ayi musu ba wai iya tawagarsa ba hatta sauran kungiyoyi da ke fuskantar yawan majinyata shi ne sauya jadawalin wasanninsu don bai wa ‘yan wasa cikakken hutu.

Rabon Alcantara da taka leda dai tun bayan canjaras din Liverpool da Everton ranar 17 ga watan Oktoba wanda ke matsayin kari kan ‘yan wasa irinsu Kaftin din tawagar wato Jordan Henderson da Virgil Van Dijk da Joe Gomez da kuma James milner baya ga Xherdan Shaqiri da Trent Alexandre-Arnold da kuma Naby Keita dukkanninsu da ke ci gaba da jinya ba kuma tare da yiwuwar dawowarsu kafin sabuwar shekara ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.