Wasanni

Ya kamata a yi nazari kan 'yan wasan da suka yi rauni a kai-Arteta

Mikel Arteta
Mikel Arteta Getty Images

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya bayyana cewa, akwai bukatar mahukuntan kwallon kafa su yi nazari game da sauya dan wasan da ya samu buguwa a kansa.

Talla

Wannan na zuwa ne a yayin da dan wasan baya na Arsenal David Luiz zai rasa wasan da kungiyarsa za ta yi da Rapid Vienna a gasar Europa a gobe Alhamis saboda jinyar buguwan da ya samu a kansa a ranar Lahadi a yayin wasansu da Wolves.

Dan wasan ya yi karo ne da takwaransa na Wolves, Raul Jimenez, inda shi ma dan wasan na Wolves ya samu tsagu a kokon kansa.

An dai caccaki Arsenal saboda yadda ta bari dan wasan ya ci gaba da murza tamaula har tsawon minti 40 duk da wannan buguwa a kansa, kafin daga bisani ta sauya shi bayan jini ya ci gaba da tsiyayo masa.

Yanzu haka Arteta na ganin cewa, lokaci ya yi da za a rika bai wa ‘yan wasan da suka samu kansu a irin wannan hali karin lokaci na hutu, sannan nan take a samu wasu ‘yan wasa na wucen gadi su maye gurbinsu, amma ba wai kungiya ta ci gaba da fafatawa da ‘yan wasa 10 ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.