Kungiyoyi 9 sun samu nasarar kaiwa zagayen gasarzakarun Turai na 2
Wallafawa ranar:
Kungiyoyi 9 ne a yanzu haka suka samu nasarar kaiwa zagayen gasar zakarun Turai na 2 da ya kunshi adadin kungiyoyi 16.
Kungiyoyin kuwa sun hada da Barcelona, Bayern Munich, Borussia Dortmund, Chelsea, FC Porto, Sevilla, Juventus, Liverpool da kuma Manchester City.
Dangane da yin zarra wajen zura kwallaye a raga kuwa, bayan kammala wasanni 5 na matakin rukunin gasar zakarun Turan, ‘yan dake kan gaba sun hada da Alvaro Morata na Juventus, Haaland na Dortmund, da kuma Marcos Rashford na Manchester United dukkaninsu da kwallaye shida-shida.
Sauran dake biye da yawan kwallayen sun hada da Berisha na Salzburg, Giroud na Chelsea, da Plea na kungiyar Borussia Moenchengladbach dukkaninsu da kwallaye biyar-biyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu