Wasanni

Mourinho ya yi watsi da masu caccakar tsarin zubin wasansa

José Mourinho, mai horas da kungiyar Tottenham
José Mourinho, mai horas da kungiyar Tottenham AFP/Thomas Coex

Mai horar da Tottenham Jose Mourinho, ya caccaki wadanda ke nuna rashin gamsuwa da fasahar da yake amfani da ita wajen tsara zubin ‘yan wasansa yayin fafata wasanni, inda ya fi maida hankali wajen tsare gida.

Talla

Yayin wata ganawa da manema labarai, Mourinho ya ce samun kason maki mafi yawan a bangaren rike kwallo ko kasafta ta dalla dalla tsakanin ‘yan wasa buri ne na masu ikirarin ilimin falsafa a duniyar tamaula amma fa ba shi ba.

Wannan cece-kuce dai ya biyo bayan wasan da Tottenham ta samu nasara kan Arsenal da kwallaye 2-0 ne, wasan da ya zama na 11 da tawagar Mourinho ke samun makin rike kwallo kasa da 36 cikin dari, daga cikin wasannin 11 kuma sun yi nasara a guda 9.

Yanzu haka Tottenham ke matsayi na 1 a gasar Premier da maki 24, biye da ita Liverpool itama da maki 24 sai dai bambamcin kwallaye, sai kuma Chelsea a matsayi na 3 da maki 22.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.