Wasanni-Kwallon kafa

PSG za su gwabza da Barcelona a matakin kungiyoyi 16 na zakarun Turai

Jadawalin wasannin zagaye na 2 na gasar zakarun nahiyar Turai.
Jadawalin wasannin zagaye na 2 na gasar zakarun nahiyar Turai. (UEFA)

Paris Saint-Germain, wadanda suka sha kashi a wasan karshe na gasar zakarun Turai a kaka mai zuwa, za su fafata da Barcelona a zagayen kungiyoyi 16 na gasar, yayin da aka hada Liverpool da RB Leipzig a jadawalin da aka yi a yau Litinin.

Talla

Bayern Munich da suka doke PSG a wasan karshe na kakar da ta wuce za su barje gumi da Lazio, yayin da zakarun 2012, Chelsea za su gwabza

An hada Manchester City, wadanda ke neman lashe kofin zakarun Turai a karon farko, za su yi karon batta da Borussia Moenchengladbach.

Juventus za su fafata da FC Porto, wadanda suka lashe kofin a 2004, yayin da Real Madrid za su gwabza da Atlanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.