Wasanni

Pogba zai ci gaba da zama a Manchester United

Dan wasan Manchester United Paul Pogba.
Dan wasan Manchester United Paul Pogba. Reuters

Akwai yiwuwar Paul Pogba ya ci gaba da zama a Manchester United har zuwa kaka mai zuwa, ganin cewa, abu ne mai wahala a tantance makomarsa a cikin watan Janairu kamar yadda dillalinsa, Mino Raiola ya sanar.

Talla

A kwanan nan ne Raiola ya ce, Pogba mai shekaru 27 na cikin hali na rashin jin dadi a Manchester United kuma ya kamata ya sauya sheka a cewarsa.

Kodayake Pogba ya jaddada jajircewarsa a kungiyar bayan kalaman dillalin nasa sun gamu da suka.

Pogba wanda kwantiraginsa zai kare a 2022 a Manchester United, ya gaza haskawa kamar yadda aka yi zato tun bayan komawarsa kungiyar akan farashin Pam miliyan 89 daga Juventus a shekarar 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.