Wasanni-Kwallon kafa

Dan wasan AC Milan ya kafa tarihin cin kwallo a cikin dakikoki 6

Wasu 'yan wasan AC Milan.
Wasu 'yan wasan AC Milan. MARCO BERTORELLO / AFP

Dan wasan gaban AC Milan, Rafael Leao ya ci kwallo mafi sauri a tarihin gasar Serrie A a jiya Lahadi, bayan da a cikin dakikoki 6 ya sanya kwallo a ragar Sassuolo a wasan da suka doke ta 2-1, abin da ya kai AC Milan saman teburin gasar, a gaban Inter Milan.

Talla

Milan, wadanda ke kokarin samun nasarar lashe gasar Serie A ne a karon farko tun bayan shekarar 2011, sun kaddamar da hari ne daga baangaren dan wasan tsakiyarsu, dan kasar Turkiya Hakan Calhanoglu, wanda ya saka wa Leao kwallo shi kuma bai yi wata wata bay a antaya ta cikin raga.

Kwallo mafi sauri da aka taba ci a gasar it ace wacce shahararren dan wasan tawagar kwallon kafar Italiya Paolo Poggi ya ci wa Piacenza a wasansu da Fiorentina a watan Disamban shekarar 2001 bayan dakikoki 8.

Milan na gaba da Inter, tawagar Antonio Conte, da ta doke Spezia 2-1, da maki guda, tazarar maki 4 ne tsakaninsu da Juvenus, wadanda suka lallasa Parma da ci 4-0 a ranar Asabar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.