Ekong da Omeruo ba su cacanci yi wa Eagles wasa ba - Babangida
Wallafawa ranar:
Tsohon dan wasan tawagar kwallon kafar Najeriya, Tijani Babangida ya ce bai kamata ‘yan wasan da ke wasa a rukuni na 2 a Turai su samu gayyata zuwa babban tawagar kwallon kafa ta kasa ba.
Talla
Babangida, wanda shine shugaban kungiyar kwararrun ‘yan wasan kwallon kafa ta Najeriya, ya bayyana hakane a wata ganwa da manema labarai ta kafar intanet.
Kenneth Omeruo, William Troost-Ekong da Jamilu Colins na cikin ‘yan wasan da ke wasa a rukuni na biyu a Turai, kuma har yanzu ke yi wa tawagar Super Eagles ta Najeriya wasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu