Wasanni-Kwallon kafa

Matsayin Benzema a harkar murza leda na dabam ne - Zidane

Karim Benzema, damn wasan Real Madrid.
Karim Benzema, damn wasan Real Madrid. REUTERS/Sergio Perez

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya bayyana Karim Benzema a matsayin dan wasan da ya ke wani matsayi na dabam a harkar murza leda.

Talla

Benzema ya ci kwallo guda, ya kuma taimaka aka saka biyu a raga a wasan da Madrid suka lallasa Eibar 3-1 a ranar Lahadi a gasar La Ligar kasar Spain.

Wannan ne karo na 30 da Benzema ya ke  taimakawa a ci kwallo bayan ya ci a cikin wasan La Liga. Cristiano Ronaldo ne kawai ya dara shi, da gudummawa har sau 44, fiye da kowane dan wasan Real Madrid a karni na 21.

Zidane ya jinjina wa namijin kokarin da Benzema ya yi bayan da Madrid ta zo daidai da Atletico Madrid a matsayi na farko a teburin La Liga da maki 29, sai dai sun fi yaran na Diego Simeone da yawan wasanni biyu.

Zidane ya ce Benzema dan wasa ne mai bai wa tawaga nasarori, kuma matsayinsa na dabam ne, ba kawai don yana cin kwallaye ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.