Wasanni

Arsenal ta huci haushin jin jikin da take yi a gasar Premier kan Chelsea

'Yan wasan Arsenal yayin murnar lallasa takwarorinsu na Chelsea a gasar Premier
'Yan wasan Arsenal yayin murnar lallasa takwarorinsu na Chelsea a gasar Premier REUTERS/Andrew Boyers

Arsenal ta kawo karshen fargabar da magoya bayanta ke yi na yiwuwar fadawarta cikin ajin ‘yan dagaji, bayan da ta lallasa Chelsea da kwallaye 3-1 a ranar Asabar.

Talla

Kafin fafatawar dai maki 3 kacal ne suka raba Arsenal da fadawa cikin ajin na ‘yan dagajin dake kasan teburin gasar Premier, sakamakon koma baya mafi muni cikin shekaru 46 da kungiyar ta fuskanta a kakar wasa ta bana.

Zalika wasan da Arsenal ta doke Chelsea shi ne farko da ta samu nasara cikin wasanni 8 da ta fafata jere da juna a kakar wasa ta bana, abinda ya ragewa kocinta Mikel Arteta matsin lambar da yake fuskanta.

Tarihi dai ya nuna sau daya Arsenal ta taba karkare gasar Premier a ajin ‘yan dagaji a kakar wasa ta 1912/1913, inda ta koma matakin gasa mai daraja ta 2 a Ingila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.