Wasanni

Mai yiwuwa Ozil ya koma cikin tawagar Arsenal a watan Janairu

Mesut Ozil
Mesut Ozil REUTERS/Edgar Su

Kwararan majiyoyi daga Arsenal sun ce an samu rarrabuwar kai tsakanin ‘yan wasan kungiyar, dangane maido da Mesut Ozil cikin tawagarsu a wata mai kamawa.

Talla

A karshen kakar wasa ta bana yarjejeniya za ta kare tsakanin Arsenal da Ozil dake karbar albashin fam dubu 350 a mako guda, wanda kuma duk da hakan kocin kungiyar Mikel Arteta ya cire shi daga tawagarsa dake buga wasannin Premier da kuma Europa a bana.

Sai dai majiyoyi daga kungiyar sun ce a watan Janairun ake sa ran maida Ozil cikin tawagar da a baya aka maida shi saniyar ware, sakamakon fama da matsalar rashin kwararren dan wasan tsakiya a kungiyar. Koda yake wasu na ganin abin da kamar wuya domin da zarar an bude kasuwar sauyin shekar ‘yan wasan, yana da damar raba gari da kungiyar ta Arsenal.

An dai kwashe makwanni ana rade-radin Ozil ya soma tattaunawa da kungiyar Fanerbache dake Turkiya, sai dai muddin ya amince da sauyin shekar, fam dubu 200 kungiyar tace za ta iya biyansa duk mako sabanin albashinsa na Arsenal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.