Wasanni

PSG ta kori mai horar da 'yan wasanta Thomas Tuchel

Thomas Tuchel tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta PSG.
Thomas Tuchel tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta PSG. REUTERS/Charles Platiau

Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta sanar da korar kocinta Thomas Tuchel a yau Talata amma ba tare da sanar da sunan wanda zai gaje shi wajen horar da 'yan wasan tawagar ba.

Talla

Tuchel wanda ke PSG tun watan Yulin 2018, tsawon lokacin da ya dauka ya kai kungiyar ga nasara a wasanni 95 canjaras a 12 da kuma rashin nasara a wasu wasanni 20 yayinda y adage kofunan Lig 1 sau 2 a 2019 da 2020 da kuma French Cup a 2020 kana French Lig shima dai a bana.

Akwai dai yiwuwar Mauricio Pochettino ya iya zamowa wanda zai maye gurbin Tuchel dan Jamus mai shekaru 47.

A kakar da ta gabata, Tuchel ya yi nasarar kai PSG ga wasan karshe inda ta sha kaye hannun Bayern Munich da kwallo 1 mai ban haushi.

Wasu bayanai sun ce taurarin Club din Neymar Junior da Kyllian Mbappe sun harzuka matuka da matakin kungiyar ta PSG.

A jawabinsa na rabuwa da Tuchel, mai club din na PSG Nasser al-Khelaifi ya yi wa tsohon kocin fatan alkhairi yayinda ya yaba matuka da kokarin da ya yi ga tawagar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.