Wasanni

Kocin Arsenal ya tabbatar da shirin sallamar wasu daga cikin 'yan wasansa

Kocin Arsenal Mikel Arteta
Kocin Arsenal Mikel Arteta REUTERS/Eddie Keogh

Mai horas da Arsenal Mikel Arteta ya tabbatar da shirin sallamar ‘yan wasansa idan aka bude kasuwar hada-hadar sauyin shekar ‘yan wasan a cikin watan Janairu.

Talla

Mai horaswar ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai a daren jiya, dangane da shirinsu na tunkarar wasa da West Brom ranar Asabar a gasar Premier.

Kocin yace aniyarsa a yanzu ita ce rage yawan ‘yan wasan dake tawagarsa ta farko domin daidaita tsarin aiwatar da dabarunsa na kai kungiyar ta Arsenal ga gaci, sai dai bai bayyana sunayen ‘yan wasan da yake shirin sallama ba, sai dai wasu majiyoyin na ganin ba za su wuce, Mesut Ozil, Kolasinac da callum Chambers ba.

A kakar wasan da ta gabata, Arteta ya jagoranci sayo ‘yan wasan da suka hada da Willian, da Gebriel da kuma Thomas Partey amma a cewarsa har yanzu kwalliya bata biya kudin sabulu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.