Wasanni

Messi ya zabi komawa PSG don hadewa da Neymar

Lionel Messi tare da Neymar lokacin atisaye a Barcelona.
Lionel Messi tare da Neymar lokacin atisaye a Barcelona. REUTERS/Albert Gea

Wasu bayanai da jaridun Brazil suka wallafa sun ce tauraro kuma kyaftin din Barcelona ta Spain Lionel Messi na shirin komawa PSG da taka leda sabanin Manchester City da kuma Inter Miami da ke zawarcinsa.

Talla

Messi mai shekaru 33 wanda ya mikawa Barcelona bukatar sauya sheka cikin watan Agustan da ya gabata, wani dan jaridan Brazil Thiago Asmar ya ce dan wasan ya fifita PSG kan sauran kungiyoyin biyu don hadewa da tsohon abokin wasansa Neymar Junior.

Cikin watan Yuni mai zuwa ne kwantiragin Messi zai kare da Barcelona yayinda tsohon kocinsa Pep Guardiola ke son hadewa da shi a Manchester City a bangare guda kuma David Becham ke son kai shi Inter Miami, sai dai dan jarida Asmar ya ce Messin yayin wata hirarsa da Neymar ta Watsap wadda ya gani da idonsa, kyaftin din na Barcelona ya ce a shirye ya ke ya zabi PSG akan sauran kungiyoyin biyu.

Messi da Neymar a tsawon lokacin da suka shafe suna taka leda karkashin Barcelona sun kafa gagarumin tarihi tare da kayarta da magoya baya ta yadda suka dage kofin lig har sau biyu gabanin Neymar ya sauya sheka zuwa PSG a 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.