Wasanni-Kwallon kafa

Ku yi hakuri da Hazard - Zidane

Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane.
Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane. REUTERS/Juan Medina

Mai horar da ‘yan wasan Real Madrid, Zinedine Zidane ya ce dole a yi hakuri da Eden Hazard, bayan da ya kasa tabuka wani abu a wasan kusa da na karshe na Supercopa de Espana da Athletico Bilbao suka dokesu 2-1 a daren Alhamis.

Talla

Kwallaye 2 a zubin farko na wasan daga Raul Garcia suka kai Bilbao wasan karshe inda za su gwabza da Barcelona, duk da cewa Karim Benzema ya zura kwallo a raga a minti na 73 na wasan.

Sau daya Hazard ya buga kwallon da ta nufi wajen mai tsaro raga kafin a cire shi a tsakiyar wasan, aka maye gurbinsa da Vinicius Junior mai shekaru 20.

Hazard dan kasar Belgium ya yi ta fama da jinyar rauni tun da ya koma Real Madrid, kuma kwallaye 2 kawai ya ci daga wasanni 10 a dukkan gasanni a wannan kaka.

Zidane ya ce dan wasan mai shekaru 30 yana bukatar lokaci don dawowa kan ganiyarsa, yana mai watsi da batun da ake cewa magoya baayan Madrid sun gaji da rashin katabus dinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.