Na gamsu da yadda Arsenal ke murza leda - Arteta
Wallafawa ranar:
Kocin Arsenal, Mikel Arteta ya bayyana jin dadinsa da yadda ‘yan wasansa suka murza leda a wasansu da Crystal Palace duk da cewa sun tashi canjaras ba kare bin damo, a daren Alhamis.
Ko da yake Arsenal din sun buga wasanni 5 a jere ba tare da sun yi rashin nasara ba, kuma sau 4 a jere kwallo ba ta taba zarensu ba, sun kasa keta bayan Palace, saboda sau hudu kawai suka buga kwallon da ta kai ga mai tsaron ragar abokan hamayyarsu tsawon mintina 90 na wasan.
Wannan ne karo na 7 da Arsenal suka kasa cin kwallo a gasar Firimiya a wannan kaka, abin da ya zo daidai da adadin wasannin da ta buga canjaras babu ci a dukannin wasannin kakar 2019-20.
Tun a kakar wasa ta 2015-16 Rabon da Arsenal su buga wasannin da suka kai wannan adadi ba tare da jefa kwallo a raga ba .
Arteta ya ce ba shakka tawagarsa ta kasa samar da damammakin cin kwallaye, amma yana mai yi musu uzuri da cewa akwai gajiya a tattare da su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu