AC Milan ta dauko tsohon dan wasan Juventus Mandzukic
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Hukumomi a AC Milan sun tabbatar kammala cinikin tsoho dan wasan gaba na Juventus, Mario Mandzukic a kan kwantiragin da zai kai har karshen wannan kaka.
Mandzukic ya yi zama a matsayin dan wasan da ba shi da kungiya tun da ya bar kulob din sa a kasar Qatar Al-Duhail a watan Yulin shekarar da ta gabata.
Dan shekara 34 din zai kara wa gaban AC Milan karfi da kwarewarsa a karkashin jagorancin shahararren dan wasan gaba Zlatan Ibrahimovic, wanda ya ke kan ganiyarsa.
Tun a shekarar 2011 tawagar koch Stefano Pioli ke neman lashe kofin gasar Serie A, kuma tana bukatar kwarewa irin ta Mandzukic.
Mandzukic ya lashe kyautar wanda ya fi zura kwallo a raga ta Scudetto har sau 4, a yayin da yake Juventus, kana ya lashe kofin Bundesliga sau 2 da na zakarun Turai 1, a lokaci da yake Bayern Munich.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu