Wasanni

FIFA ta tabbatar da haramcin wasanni 10 kan Trippier na Atletico

Dan wasan Atletico Madrid Kieran Trippier.
Dan wasan Atletico Madrid Kieran Trippier. Reuters

Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta daukaka kara gaban kotun hukunta laifukan wasanni ta CAS kan matakin hukumar FIFA da ke tabbatar da hukunin haramcin wasanni 10 ga dan wasanta Kieran Trippier.

Talla

Tun farko hukumar FA ce ta fara zartaswa da dan wasan haramcin doka wasanni 10 amma Ateltico Madrid ta daukaka kara gaban FIFA inda aka dakatar da hukuncin na wucin gadi, gabanin shari’a.

Sai dai a zaman shari'ar da FIFA ta gudanar jiya Litinin ta tabbatar da hukuncin farko kan Trippier ko da ya ke  daukaka karar da Atletico zai bai wa dan wasan mai shekaru 30 damar ci gaba da taka leda har zuwa lokacin da za a kammala shari’a.

Matukar dai hukuncin kan Trippier ya tabbata kenan ba za a sake ganin kafarsa a fili ba har sai ranar 28 ga watan Fabarairu inda zai rasa wasannin La Liga 8 da na zakarun Turai.

Yayin zaman shari'ar da FIFA ta yi, hukumar ta ce FA na da damar zartas da hukuncin kan dan wasan la'akari da cewa ya aikata laifin ne lokacin yana taka leda a karkashin Firimiya wadda ta ke bisa kulawarta, hukuncin da FIFA ta ce zai yi aiki ba kadai a Ingila ba.

Kieran Trippier dai hukumar FA ta sameshi da laifin fallasa wasu asiran cacar wasa lokacin yana taka leda a Tottenham.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.