Wasanni-Kwallon kafa

Messi ya 'tsallake rijiya da baya' bayan jan kati

Zakara kuma Kaftin din tawagar Barcelona Lionel Messi
Zakara kuma Kaftin din tawagar Barcelona Lionel Messi Manu Fernandez/Reuters

Lionel Messi ya tsallake rijiya da baya wajen kauce wa dakatarwar wasanni da dama, bayan da ya samu jan kati na farko tunda ya fara yi wa Barcelona wasa, inda yanzu haka dan kasar Argentina din zai fuskanci horon dakatarwa na wasanni 2 bayan da aka kore shi a wasan Super Cup tsakaninsu da Atletico Bilbao, amma fa kungiyarsa za ta daukaka kara.

Talla

Hukumar da ke kula da batutuwan da suka shafi da’ar ‘yan wasa a Spain ta zartas cewa gwarzon dan kwallon ba zai sha horon dakatarwa na wasanni masu yawa ba akan laifin farmakin da aka ce ya kai wa dan wasan Bilbao, Asier Villalibre.

Da farko an tsegunta cewa Messi na iya shan horon dakatarwa na wasanni 12 sakamkon laifin da ya aikata, amma jami’an wasan tun da farko sun ce babu wani aibi a abin da ake zargin dan wasan da aikatawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.