Wasanni

Sauyin shekar Alaba daga Munich zuwa Madrid ta tabbata

David Alaba
David Alaba AFP

Majiyoyi kwarara daga Spain sun ce sauyin shekar David Alaba daga Bayern Munich zuwa Real Madrid a kakar wasa ta badi ya tabbata.

Talla

Rahotanni sun ce dan wasan mai shekaru 28 zai dafe albashin euro miliyan 11 duk shekara a Real Madrid, a karkashin yarjejeniyar tsawon shekaru 4.

Masu fashin baki kan tamaula dai sun bayyana sayen Alaba da Madrid tayi a matsayin farar dabara ta karfafa bangaren tsaron bayanta, la’akari da cewar har yanzu babu tabbas kan cigaba da zaman Sergio Ramos tare da kungiyar nan gaba, ganin cewa yana neman a tsawaita yarjejeniyarsa dake shirin karewa a bana da adadin shekaru 2, yayin da Madrid ke masa tayin shekara 1.

A gefe guda kuma sabon mai tsaron baya Eder Militao da Madrid din ta sayo daga FC Porto a 2019 har yanzu ya gaza nuna alamun kungiyar za ta iya dogara kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.