Wasanni

Karamar kungiya ta raba Real Madrid da gasar Copa del Rey

Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane.
Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane. REUTERS/Sergio Perez

Mai yiwuwa makomar kocin Real Madrid Zinaden Zidane ta sake shiga hali na rashi tabbas, bayan ficewar da suka yi daga gasar Copa Del Rey, sakamakon doke su da kungiyar Alcoyano tayi da kwallaye 2-1.

Talla

Kungiyar ta Alcoyano dai na buga wasanninta ne a mataki na 3 a gasar kwallon kafar Spain wato Segunda B a turance, abinda ya janyowa Real Madrid da kocinta Zidane caccaka, la’akari da cewar akwai manyan wasansa da suka hada da Kroos, Casemiro, Benzema da kuma Hazard, da suke kan fili a lokacin da suka sha kayen.

Karo na biyar kenan tun shekarar 2001 da wata karamar kungiya daga mataki na kasa a gasar kwallon Spain ke fitar da Real Madrid daga Copa Del Rey, gasar da Madrid din ta lashe kofinta sau 19, sai dai rabon da ta sake daukarsa yau shekaru 7.

Yanzu haka dai Zidane na fuskantar matsin lambar lashe gasar La Liga, wadda Madrid ke matsayi na biyu da maki 37, maki 4 tsakaninta Atletico Madrid, wadda ke da kwantan wasanni har guda biyu, yayin da kuma Barcelona babbar abokiyar hamayyar Real din ke biye da ita a matsayi na 3 da maki 34.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.