Wasanni

Ronaldo ya kafa tarihin zarce duk wani mai tamaula yawan kwallaye

Cristiano Ronaldo.
Cristiano Ronaldo. REUTERS/Alberto Lingria

Cristiano Ronaldo ya zama dan wasan da mafi yawan kwallaye a tarihin duniyar tamaula, bayan da ranar Laraba ya jefa kwallo guda a wasan karshe na gasar cin kofin Italiya da Juventus ta doke Napoli da 2-0.

Talla

A halin yanzu adadin kwallayen da Ronaldo ya ci a kungiyoyin da ya haskawa da kuma tawagar kwallon kafar kasarsa sun kai 760.

Ronaldo mai shekaru 35 ya zura daruruwan kwallayen ne cikin jumillar wasanni dubu 1 da 40 da ya buga a hukumance, da suka hada da kwallaye 450 da ya ciwa Real Madrid, 118 a Manchester United, 102 da ya ciwa kasarsa Portugal, 85 a Juventus sai kuma 5 a Sporting Lisbon kungiyar da ya soma haskawa.

A yanzu haka dai rahotanni sun ce Ronaldo na daukar makudan kudaden da ya zarta adadin da kungiyoyin Seria 4 ke samu a Italiya duk shekara.

Tun bayan kulla yarjejeniya da Juventus a 2018 Ronaldo ke daukar albashin kimanin fam dubu 540 a duka mako, sama da fam miliyan 2 kenan a wata guda, kudaden da in aka tattarasu tsawon shekara suka yi daidai ko dara kudaden da kungiyoyin Udinese, Verona, Spezia da Crotone ke kashewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.