Ronaldo zai iya rusa tarihin da aka kafa na cin kwallaye kuwa?

Cristiano Ronaldo.
Cristiano Ronaldo. REUTERS/Alberto Lingria

A daren Laraba Cristiano Ronaldo ya ci kwallonsa ta 760 a wasan Super na Italiya da kungiyarsa Juvenstus suka samu nasara 2-0 a kan Napoli, abin da ya sake tada ikirarin cewa shine dan kwallon da ya fi saka kwallaye a raga a duniya. Sai dai akwai takaddama a kan waye ya fi cin kwallaye a duniya.

Talla

Ronaldo ya nuna bajinta, inda a matsayinsa na matashin dan wasa, ya ci wa Lisbon kwallaye 5, ya koma Manchester United ya ci kwallaye 118, ya ci 450 a Real Madrid, 85 a Juventus, sai kuma 102 a tawagar kwallon kafar Portugal.

Dan wasan gaban na tawagar kwallon kafar Portugal, wanda a wata mai kamawa zai cika shekaru 36, ya kafa tarihi a harkar kwallon kafa a bangarori da dama. shi ne dan wasan da ke kan gaba a cin kwallaye a Real Madrid da kuma kasarsa, kuma yana gaban Lionel Messi a cin kwallaye a gasar zakarun nahiyar Turai.

Sai dai ana ci gaba da kokwanto a kan ko Ronaldo din ne ke kan gaba a harkar kwallon kafa gaba daya wajen yawan kwallaye, saboda ‘yan wasan Brazil Pele da Romario na ikirarin cewa sun ci sama da kwallaye dubu daya.

A watan da ya gabata, Lionel Messi ya zarta kwallaye 643 da aka amince da su a hukumance cewa Pele ya ci wa kungiya guda, amma ba tare da bata lokaci ba Santos na Brazil, inda Pele ya yi wasa suka ce gwarzon dan kwallon da ya lashe kofin duniya har sau 3 ya ci musu kwallaye dubu 1 da 19 idan aka hada da wasannin sada zumunta.

Bayanin Pele a shafinsa na Instagrm na nuni da cewa shine ya fi kowa saka kwallaye a raga a harkar kwallon kafa a duniya, da kwallaye dubu 1 da dari 2 da 83.

Sai dai kuma, idan wasanni da aka yi a hukumance ne abin la’akari, dan kasar Brazil din, wato Pele yana bayan Josef Bican, wanda masana tarihin kwallon kafa suka yi ittifakin cewa ya ci kwallaye 805 a cikin wasanni 530 a tsakanin shekarun 1931 da 1955, inda ya buga wa kungiyoyi 6 da kuma kasashen Austria da Czechoslovakia.

Pele ya ci kwallaye tsakanin 757 da 767 a wasannin da ya yi a sana’arsa ta kwallon kafa da suka hada da 92 da ya ci wa kasarsa Brazil.

An sanya shi a matsayin na 3 a bayan wanda ya taimaka wa Brazil a gasar kofin Duniya ta 1994 mai kwallaye 772 Romario.

A shekarar 2007 Romario ya yi bikin kai wa kwallaye dubu 1, adadin da ya hada da kwallayen da ya ci tun yana matashin dan wasa da kuma wasannin sada zumunta da na karramawa.

Shi ko Messi, wanda shekarunsa 33 yana da kwallaye 719 wandanda ya ci wa Barcelona da Argentina kuma yana iya cimma ma wadanda ke gabansa kafin ya yi ritaya.

Sai dai abin da ake kyautata zato a nan shi ne, ko da Ronaldo bai kafa tarihin zama dan wasan da ya fi kowa zura kwallo a raga ba a yanzu, akwai alamun cewa zai cimma haka a matsayinsa na dan wasan da ke ci gaba da cin kwallaye duk da cewa yana daf da cika shekaru 36 da haihuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.