Wasanni

UEFA ta bayyana tawagar fitattun 'yan wasanta a 2020

Tawagar zababbun 'yan wasan hukumar UEFA na shekarar 2020.
Tawagar zababbun 'yan wasan hukumar UEFA na shekarar 2020. YouTube/UEFA tv

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai UEFA, ta fitar da jerin ‘yan wasan da masoya kallon tamaula suka zaba mata, a matsayin tawagar fitattun ‘yan wasanta na shekara.

Talla

UEFA ta baiwa masoya kwallon kafa damar soma kada kuri’unsu wajen zaba mata tawagar ‘yan wasan 11 ne daga ranar 30 ga watan Nuwamba zuwa 6 ga Janairun da muke, inda ‘yan wasan Bayern Munich suka fi na kowace kungiya yawa.

Tawagar ta shekarar 2020 ko kakar wasan da ta kare, ta kunshi Manuel Neuer na Bayern Munich a matsayin mai tsaron raga.

Masu tsaron baya kuma sun hada da Joshua Kimmich, da Alphonso Davies dukkaninsu daga Bayern Munich, sai kuma Sergio Ramos na Real Madrid da Virgil van Dijk na Liverpool.

A bangaren ‘yan tsakiya masu tare akwai Kevin de Bryune na Manchester City da Thiago Alcantara na Bayern Munich, yayin da kuma mahara suka hada da Lionel Messi na Barcelona, Cristiano Ronaldo na Juventus da kuma tauraron PSG wato Neymar.

Gwarzon dan wasan duniya na FIFA Robert Lewondoski masoya tamaula suka zaba a matsayin lamba taran tawagar kwallon kafar hukumar ta Turai UEFA.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.