Wasanni-Coronavirus

Japan ta musanta dakatar da gasar Olympics

Wasu mata yayin atsaye a gaban alamar gasar Olympics dake gaf da babban filin wasa na Tokyo, babban birnin kasar Japan. 22/1/2021.
Wasu mata yayin atsaye a gaban alamar gasar Olympics dake gaf da babban filin wasa na Tokyo, babban birnin kasar Japan. 22/1/2021. REUTERS/Kim Kyung-Hoon

Gwamnatin Japan ta musanta rahotannin dake cewa ta soke gasar Olympics da aka tsara za ta gudana a ranar 23 ga watan Yuli mai zuwa, bayan dakatar da ita da aka yi a shekarar 2020 saboda annobar coronavirus.

Talla

A watan Maris da ya gabata aka tsara gasar ta Olympics za ta gudana a birnin Tokyo amma aka dage ta bisa tilas saboda barkewar cutar Korona, wadda ta tilastawa daukacin wasanni da sauran harkoki tsayawa cik tsawon watanni a shekarar bara.

Rashin tabbas kan yiwuwar gasar wasannin motsa jikin ta Olympics dai ya biyo bayan sake bayyana da annobar ta Korona ta yi a sassan Japan, inda a yanzu haka mafi akasarin yankunan Tokyo babban birnin kasar ke karkashin dokar kulle ko kuma takaita zirga-zirga.

Sai dai cikin sanarwar da suka fitar a yau Juma’a, masu ruwa da tsaki wajen shirya gasar sun ce tsare-tsare na cigaba na gudanar wasannin na Olympics a watan Yuli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.