Wasanni

Ahmed Musa zai kulla yarjejeniya da West Brom

Kaftin din Najeriya Ahmed Musa
Kaftin din Najeriya Ahmed Musa REUTERS/Toru Hanai

Kaftin din tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagle Ahmed Musa, na shirin kulla yarjejeniya da kungiyar West Brom dake gasar Premier Ingila.

Talla

Rahotanni sun ce ana sa ran ranar Larabar nan dake tafe Musa zai yi tattaki zuwa Ingila domin tantance lafiyar sa kafin rattaba hannu kan yarjejeniyar da majiyoyi suka ruwaito cewar bai mai tsawo bace.

A halin yanzu kungiyar West Bromwich Albion ce ta 19 a gasar Premier da maki 11.

A shekarar 2016 Ahmed Musa ya rabu da CSKA Moscow dake Rasha, bayan ci mata kwallaye 55 a wasanni 167 da ya buga mata, inda ya koma kungiyar Leicester City a shekarar.

Bayan rashin gajeren likaci a Leicester Ahmad ya sako komawa CSKA Moscow kan aro, daga nan kuma ya koma Al Nassrr dake Saudiya a Janairun 2019, inda a watan Oktoban bara ya rabu da kungiyar, kawo yanzu kuma ba ya tare da wata yarjejeniya, sai wadda yake shirin kullawa da West Brom.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.